Monday, July 23, 2018

Labaran duniya :: Ambaliya ta kashe mutum 13 ta raba 17,000 da muhallansu a Nijar

Tags

A kalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu wasu 13 kuma suka jikkata sakamakon ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta shatatawa a 'yan kwanakin nan a jihohin Maradi, Agadez da kuma Diffa a Jamhuriyar Nijar.
Wata sanarwa da hukumar agajin gaggawa ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ta fitar ta ce, wasu mutanen da yawansu ya kai 17,000 sun rasa muhallansu.
Sanarwar ta ce a ranar 18 ga wannan wata na Yuli ruwan sama ya hadassa asarar rayuka da ta dukiyoyi a wasu yankunan kasar.
An kiyasta cewa eka 400 ta kasar noma ta lalace sannan dabbobi 24,000 sun mutu sakamakon ambaliyar.
Ambaliyar Katsina: Ruwa ya tafi da jaririya 'yar wata uku
An hana 'yan agajin kungiyar Izala sa inifom a Nijar
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 40 a Katsina
A tsakiyar watan da ya gabata ne dai hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar Jamhuriyar Nijar ta fuskanci matsalar ambaliyar da ka iya shafar a kalla mutum 170,000 a jihohin Dosso da Niamey, inda kogin Nijar ya ratsa.
Duk da cewa daminar wata uku kadai ke yi kuma ba a samun ruwa mai yawa, kasar na fuskantar matsalar ambaliya a 'yan shekarun baya-bayan nan.
Ko a shekarar da ta gabata ma mutum sama da 50 suka gamu da ajalinsu biyo bayan ambaliyar ruwa, yayin da wasu 206,000 suka rasa matsugunansu,sannan heka 9800 ta kasar noma ta salwanta.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce ta saka makudan kudade da kusan CFA biliyan uku tare da taimakon Bankin Duniya don gina shingayen da za su hana kwararar ruwan zuwa gidajen da ke bakin kogin Nijar a Yamai, a matsayin riga-kafi.
Gwamnatin dai ta ce tuni ta kamala wannan aiki.

Pharmaceutical company


EmoticonEmoticon

Facebook