Wednesday, November 21, 2018

Labaran duniya ::: Ku kalli kifin da ya hadiye kilo shida na robobi

Tags

Jami'ai sun ce an gano wajen kilo shida na robobi a cikin wata matacciyar giwar teku wadda ruwa ya turo ta gabar teku a wani gandun daji da ke Indonesia.
An gano kofunan roba 115 da robobin ruwa hudu da ledoji 25 da kuma takalman roba biyu a cikin giwar tekun.
An gano gawar giwar tekun mai tsawon mita 9.5 a cikin tekun da ke kusa da tsibirin Kapota a gundun dajin Wakatobi a ranar Litinin.
Ana binciken halittun da matukiyar jirgi ta gani a sama
Biri ya kashe wani jariri a Indiya
Kifi ya kashe wani mutum bayan ya cece shi
Gano giwar tekun ya haifar da damuwa tsakanin masu fafutukar kare muhalli.
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ce Dwi Suprapti, wata jami'a da ke kare hakkokin dabbobin ruwa a WWF a Indonesia, ta ce: "Ko da yake ba mu iya gano dalilin mutuwar giwar tekun ba, amma abubuwan da muka gani da idanuwanmu ba su da kyawun gani."
Ta kuma kara da cewa ba zai yiwu a ce robobin da giwar ta hadiye ne dalilin da ya haifar da mutuwar giwar ba saboda yanayin rubewar da ta yi.
A cikin wani sakon da asusun tallafin gandun daji WWF ya wallafa a shafinsa na Twitter ya yi bayani dalla-dalla kan abubuwan da aka gano a cikin dabbar:
"Roba mai karfi (guda 19 mai nauyin giram 140) da kwalaben roba (guda 4 masu nauyin giram 150) da jakankunan roba (guda 25 masu nauyin giram 260) da takalman roba (guda 2 masu nauyin giram 270) da zararruka masu nauyin kilogiram 3.26 da kuma kofunan roba (guda 115 masu nauyin giram 750). "

Pharmaceutical company


EmoticonEmoticon

Facebook