Wednesday, November 21, 2018

Labaran siyasa :: 'Yan sandan Najeriya sun gargadi APC da PDP

Tags

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta gargadi 'yan siyasa na jam'iyyu daban-daban ciki har da APC da PDP su guji tayar da husuma lokacin yakin neman zaben 2019.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood ya aike wa manema labarai ta babban sufeton 'yan sandan kasar Ibrahim Idris, ya ce zai dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin zaben ya gudana ba tare da tashin hankali ba.
"Muna bai wa dukkan jam'iyyu umarni da su yi biyaya ga dokokin zabe. Su tabbatar sun gargadi masu yin takara a karkashinsu da masu goyon bayansu da kada su tayar da tarzoma" idan ba haka ba za su dandana kudarsu.
PDP ta zargi APC da 'murkushe abokan hamayyar siyasa'
Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari
Nigeria: An sassari mutane a hawan Daushen Kano
Mr Moshood ya kara da cewa babban baturen 'yan sandan kasar ya umarci kwamishinonin 'yan sandan kasar 36 da na Abuja da kuma mataimakansa na shiyya 12 su tabbatar da tsaro a wuraren yakin neman zabe.
Kazalika, rundunar ta umarci 'yan sandan su guji shiga harkokin siyasa domin su kare martabarsu.
"Rundunar 'yan sanda ba za ta lamunci yin kalaman batanci da na tayar da husuma wadanda ka iya haddasa tashin hankali daga kowanne mutum lokacin yakin neman zabe da bayan sa ba,' in ji Mr Moshood.
A cewarsa, dole sarakuna da iyaye su ja kunnuwan 'ya'yansu game da shiga bangar siyasa, yana mai cewa rundunarsu za ta hukunta duk mutumin da aka samu da hannu wurin tayar da hankali.
Ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka soma yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya.
'Yan takara sama da 30 ne za su fafata a zaben shugaban kasar, ko da yake masu sharhi na ganin fafatawar za ta fi yin zafi tsakanin Alhaji Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wanda ke son yin wa'adi na biyu na mulki.
Karin labaran da za ku so ku karanta

Pharmaceutical company


EmoticonEmoticon

Facebook