Thursday, July 27, 2017

Tags

DIGIRIN girmamawa ko ince digirin digirgir da Annabi (SAW) ya baiwa Sahabansa da bakinsa kamar haka TARE DA REFFERNCES

1.wanda ya fi kowa tausayin al,ummata shi ne ABUBAKRIN ASSIDDEEQ

2.Wanda ya fi kowa karfi acikin addini (wanda ba ya bari ataba addinin ALLAH) shi ne UMAR

3.Wanda ya fi kowa jin kunya shi ne: USMAN

4.Wanda ya fi kowa sanin hukunce-hukunce (alkalanci) shi ne ALI

5.Wanda ya fi kowa iya karatun Qur,ani shi ne UBAYYU BIN KA,AB

6.Wanda ya fi kowa sanin halal da haram shi ne MU,AZU BIN JABAL

7.Kowace al,umma ta na da Amini, Aminin wannan al,umma shi ne ABU UBAIDA BIN JARRAH

8.Wanda ya fi kowa sanin ilimin rabon gado shi ne: ZAIDU BIN
SABIT

9.Kowanne Annabi ya na da mataimaki AZZUBAIR kaine mataimakina

10.Wanda ya ke son yayi karatun Qur,ani kamar yadda aka saukar da shi, to yayi salon karatu irin na ABDULLAHI BIN MAS,UD

11. HASAN da HUSAINI su ne shugabannin matasan gidan Aljannah

12.Shahidi wanda ya ke tafiya a ban qasa shi ne DALHATU BIN UBAIDULLAH

13.Na fansheka da iyayena SA,AD BIN ABI WAQQAS

14.Haqiqa ALLAH YA riqeni khalilinsa kamar yadda ya riqi Ibrahim khalil, gidana da na Ibrahin suna kallon juna a aljanna, ABBAS kuma ya na tsakaninmu, mumini atsakanin badadayai kenan

15.Maraba da tsarkakakke kuma abun tsarkakewa AMMAR BIN YASIR

16 ALLAH YA umarceni da inso mutum hudu kuma shi ma ya na sansu:ALI, DA ABU ZARRIN ALGIFARIYY, DA SALMANUL FARISIY, DA MIQDAD

17.Qasa ba ta taba daukar mutumin da, haka kuma sama bata taba rufe mutumin da yafi kowa gaskiyar magana kamar ABU ZARRIN ALGIFARIYY BA

18.Mayafinsa na gidan aljanna ya fi mayafin alhariri, haka kuma al,arshi yayi girgiza sabo da rasuwar SA,AD DAN MU,AZ

19.Ya ALLAH KA tabbatar da shi kuma ka sanya shi shiryayye mai shiryarwa: JARIR DAN ABDULLAH ALBAJALIY

20.Ya ALLAH KA sanar da shi hikima da fassarar Qur,ani ABDULLAHI DAN ABBAS

21.Wanda ya so MUTANEN MADINA Allah zai so shi wanda kuma ya qisu shima Allah zai qishi

22.Zababbun cikinmu kenan: WADANDA SU KA JE YAKIN BADAR
***************************
( DUK WADANNAN BAYANAN
DUBA LITTAFIN IBN MAJA BABUN FI FADHA,ILI AS,HABI RASULULLAHI (SAW))

23. Ya BILAL bani labari da mafi fatanka a ayyukan da ka aikata a musulunci dan haqiqa ni na ji sautin takalminka a gabana a gidan aljannna,,,,,,,,,,,,,,,.

*****(Bukhari 3679)******

24. Abubakr dan aljannane,
Umar dan aljannane,
Usman dan aljannane,
Ali dan aljannane,
Dalha dan aljannane,
Zubair dan aljannane,
Abdur-Rahman Bin Auf dan aljannane,
Sa,ad bin Abi waqqas dan aljannane,
Sa,id bin Zaid dan aljannane,
Abu Ubaidah bin Jarrah dan aljannane,

*******(Duba Tirmiziy 3748)****

25. Kada ku zagi sahabbaina wallahi da ace dayanku zai ciyar da misalin dutsen uhudu na zinare to da bazai kai mudun dayansuba, kai ba ma zai kai rabin nasuba (awajan girman lada)

*****(Bukhari da Muslim) ******

Muna rokon ALLAH wadannan sahabbai dama wadanda bamu ambataba ALLAH YA qara musu yarda,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, Inkaturashi xuwa gah wani/group domin 'yan

uwanka sugani sukaru wace hasara kayi?
ALLAH YASA muyi kyakkyawan karshe!
AMEEN


EmoticonEmoticon

Facebook