Thursday, July 27, 2017

Duniyar mu a yau

Tags

KYAUTAR ALLAH TAFI TA KOWA
Akwai wani sarki a kasar Habasha kullum idan ya fito zaure sai ya sami wasu mabarata wato masu bara guda biyu a kofar zaure. Kullum idan sarki ya fito sai yaji mabaraci na farko yana cewa "KYAUTAR SARKI TAFI TA KOWA" sai mabaraci na biyun kuma yace "KYAUTAR ALLAH TAFI TA KOWA", idan sarki kuma yaji zancen na farkon sai yaji dadi, amma idan yaji zancen mabaraci na biyun sai ransa ya baci.
.
Ana nan a haka rannan sarki ya fito zaure kamar yadda ya saba, fitarsa keda wuya sai yaji mabaratan sunzo yin bararsu kamar yadda suka saba, mabaraci na farko yace "KYAUTAR SARKI TAFI TA KOWA", na biyu kuma ya amsa "KYAUTAR ALLAH TAFI TA KOWA", sarki yana jin haka sai ya kira mabaraci na farko wato wannan mai cewa kyautar Sarki tafi ta kowa, sarki ya shiga ya dauko wani abu kamar gurasa ya baiwa mabaracin, bayan mabaracin ya fito ya sami dan uwansa a tsaye a waje sai ya nunawa dan uwan nasa gurasar da sarki ya bashi, sa'annan ya fadawa dan uwan nasa cewar shi ya zata ma kudi sarki zai bashi saboda yafi son kudi, daga nan ya sayarwa mabaraci na biyun gurasar akan fam biyar.
Bayan mabaraci na biyun ya koma gida ya dauki gurasar domin yaci, bude cikin gurasar keda wuya sai yaga ZINARI a cike a cikin gurasar, cikin farin ciki ya daga hannunsa sama ya godewa Allah yana mai cewa "KYAUTAR ALLAH TAFI TA KOWA".
Washe gari sarki ya fito zaure kamar yadda ya saba sai yaji mabaraci na farko yana cewa "KYAUTAR SARKI TAFI TA KOWA" sarki ya jira yaji muryar mabaraci na biyu kamar yadda ya saba amma baiji ba, sai ya fito ya leka ya tambayi mabaraci na farkon ina dan uwansa ? Sai yacewa sarki "NI BAN GASHI BA YAU, KUMA BAN SAN GIDANSA BA, DAMA A KOFAR GIDAN NAN MUKA SABA HADUWA SAI MU SHIGO TARE.
Sarki yace "Amma ga alama dai baka bude cikin gurasar dana baka jiya ba har yanzu ko ? Mabaracin ya risina yace "RANKA YA DADE BANCI BA, HASALI MA NAFI BUKATAR KUDI NE SHI YASA NA SAYARWA DAN UWANA MABARACIN NAN GURASAR"
Sarki ya dafe kai yace "Kash ! Baka da rabo, ai na sanya maka Zinari a ciki saboda in gaskata zancenka cewar KYAUTAR SARKI TAFI TA KOWA", koda mabaracin yaji haka sai ya fadi ya suma, sarki kuwa cikin sanyin jiki yace "HAKIKA KYAUTAR ALLAH TAFI TA KOWA"
.
ALLAH KA BAMU KYAUTAR NI'MARKA A DUNIYA SA'ANNAN KA SANYAMU CIKIN DAUSAYIN RAHMARKA A KIYAMA...


EmoticonEmoticon

Facebook