Wednesday, July 12, 2017

Islamic

Tags

Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA, ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM, WHATSAPP, da sauransu.


Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.


Manzon Allah (s.a.w.w) yace: *"WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA*
*ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"*


Wani mutum yazo wajen manzon Allah S.A.W.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.


1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa."


2. Ina son in zama mafi arziQi a cikin mutane?
AMSA
sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci."


3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa."


4. Menene zai kare ni daga wuta?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi."


5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka."


6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah."


7. Ina son imanina ya zama ingantacce?
AMSA.
Sai ya ce "Ka gyara halayen ka."


8. Menene yake huce fushin Allah (S.W.T.)?
AMSA
Sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata ma 'yan uwa."


9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Mummunar hali shine rowa"


10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah."


YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya.


INA ROQON MAI KARATU dan GIRMAN ALLAH DAN SON ANNABI kayi Qokari ka tura wani group d'in domin tunasarwa.


EmoticonEmoticon

Facebook